Majalisar dattawan Amurka ta kira Bush ya janye dakarunsa a shekara mai zuwa | Labarai | DW | 23.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattawan Amurka ta kira Bush ya janye dakarunsa a shekara mai zuwa

Majalisar dattawan Amurka ta amince da fidda dala biliyan 22 domin daukar nauyin yaki Iraqi da Afghanistan,sai dai kuma tayi kira ga Shugaba Bush daya janye dakarunsa daga Iraqin a farkon shekara mai zuwa.

Kodayake fadar gwamnati ta white house tayi barazanar yin nafani da ikonta na darewa kujerar naki game da wannan batu.

Yan jamiyar demokrats sunce janyewar sojojin Amurka daga Iraqi zai baiwa yan kasar ta Iraqi damar naukar nauyin harkokin tsaro a kasarsu.

Sun bukaci dakarun Amurka su fara janyewa cikin watanni hudu da zummar kammala janyewar zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2008.

Majalisar wakilai ta Amurkan tana duba kudurin doka mai kamar haka