1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dattawa ta kara wa'adin dokar ta-baci

May 20, 2014

A wani abun dake zaman kokari na kara kwarin gwiwa ga shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, majalisar dattawan kasar tabi sahjun ‘yar uwarta ta wakilai wajen amincewa da dokar ta baci a Yobe da Adamawa da Borno

https://p.dw.com/p/1C3Tz
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A wani abun dake zaman kokari na kara kwarin gwiwa ga shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan dake kara fuskantar hare-hare ta ko ina cikin kasa, majalisar dattawan kasar tabi sahjun ‘yar uwarta ta wakilai wajen amincewa da karin wattani shida a bisa dokar tabacin kasar ta shekara guda.

Sun dai kuma sai da yan majalisar suka kai ga sauka daga dokin naki kuma sun kai ga sauyin matsayi, ga ‘ya'yan majalisar dattawan Tarrayar Najeriyar da ranar yau suka bi sahun ‘yan uwansu na wakilai wajen amincewa da karin wattani shida a bisa dokar tabbacin kasar ta Najeriya.

Dattatwan da suka share tsawon awoyi uku suna wata gannawar sirri tsakaninsu da shugaban majalisar dattawan dai basu kai ga bata lokaci ba wajen kaiwa ga amincewa kan dokar da a baya dattawan arewacin kasar suka ce akai ga kasuwa kanta.

Matakin dattawan dai ya kai ga kara kwarin gwiwa ga shugaban dake dada fuskantar matsin lamba a ciki da waje, dama karin hare-hare daga kungiyar ta Boko Haram dake dada samun karfi na rawar gaban hantsi cikin kasar.

Senata Umar Dahiru dai na zaman shugaban kungiyar dattawan arewacin kasar da a baya suka kekasa kasa suka nuna adawar su bisa matakin da suka ce yayi kama da siyasa a cikinsa, kuma a fadarsa sauyin matsayin nasu na zaman bisa sharuda ga gwanatin ta Abuja.

“ An fadi sharuda da dole a cika su, alal misali wuraren nan da ake fadace-fadace wadanda aka nakasasu dole ne shugaban kasa yazo da kasafi na taimakonsu, ba shi kadai ba, sojojin dake aiki kara zube dole sai an basu kayan aiki aikin banza ne da basu da makamai”

Akalla sharuda guda takwas din da suka hada da baiwa majalisar rahoto na wata- wata, da kuma shigar da 'yan kungiyar farar hular Civilian JTF ya zuwa aikin soja dai ne ya kai ga sauyin matsayin da majalisar tace tana iya soke dokar da zarar an kai ga karkace hanya a bisa alkawari a fadar Senata Ali Ndume dake zaman daya a cikin dattawan da suke wakilar yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya.

Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

“Kuskuren da akai da shine an basu wata shida ba 'a bincika me akai, mun canja wannan yanzu kowane wata sai an zo gaban majalisa an bamu bayani akan nawa aka basu, me suka yi dashi wsane gari suka kama da sauran bayanai da zasu yi gaban majalisar dattawa”

Tuni dai fadar gwamnatin kasar ta fara kokarin cika burin dattawan tare da kakakin fadar, sannan da wasu jeri na matakan da suka hada da bada tallafi na musamman ga al'ummar da rikicin ya kai ga tagayarawa da kuma bada karin kariya cikin makarantu dake daukacin yankin a fadar Reuben bati dake zaman kakakin fadar.

“Sabon shirin zai kunshi kai karin kaya na agaji ga kananan hukumomin da rikicin ya shafa da suka hada da kayan abinci da magunguna da kuma kayan agaji da ma kudi ga iyalin da abun ya shafa. Bayan nan shugaba Jonathan ya bada umarnin kara gaggauta nazarin bukatun mutanen da annobar ta kai ga rutsawa domin gano garruruwa da mutanen da abun ya shafa da kuma irin asara ta rayuka da dukiya da aka samu. Bayan nan kuma shugaban kasa ya bada umarnin karin kariya ga makarantun Borno da sauran sassa na kasa da kuma bada agajin da zai sa dalibai komawa cikin aji don cigaba da karatu”

Sabbabin matakan dai na zuwa ne dai dai lokacin da ake sa ran akalla bataliya guda na sojan kasashen dake makwabta da Tarrayar Najeriya ne dai zasu bi sahun na kasar ta Najeriya kusan dubu 20 a cikin yakin da sannu a hankali ke daukar fasalin sanda da karas ga kasar da abaya tace bata shirin tattaunawa da masu sana'ar ta'addanci.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria
Hoto: DW

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu