Majalisar Amirka ta yi fatali da bukatar Trump | Labarai | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Amirka ta yi fatali da bukatar Trump

Majalisar dokokin Amirka ta yi watsi da bukatar shugaban kasar na rusa shirin Inshorar lafiyar da tsohon shugaba Barack Obama ya kafa da aka fi sani da 'ObamaCare'

Shugaba mai ci Donald Trump ne dai ya bukaci yi wa shirin na inshorar lafiya wato 'ObamaCare' garambawul, watsin da kuwa a yanzu ake ganin wani babban cikas ga gwamnatin kasar ta yanzu.

'Yan majalisar Amirkar da suka kunshi 'yan jam'iyyar Republican ta shugaba Trump ciki har da Sanata John McCain sun taka rawa wajen kashe batun a muhawarar da aka yi a wannan Juma'a.

Sanatoci 51 cikin 100 da ake da su ne dai suka zabi watsi da batun da jijjifin safiyar Juma'ar.