Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake ƙaƙabawa Koriya ta arewa takunkumi. | Labarai | DW | 07.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake ƙaƙabawa Koriya ta arewa takunkumi.

Gaba ɗaya manbobin kwamitin guda 15 ,suka amince da daftarin ƙudirin a kan Koriya ta arewa, sakamakon gwaje gwaje na makaman nukiliya da ta yi.

Kwamitin sulhu na MDD ya kaɗa kuri'a amincewa da , da daftarin kudiri ne da ke tsaurara takunkumin karya tattalin arziki ga ƙasar Koriya ta arewa.Dangane da gwaje gwaje makamai masu ci dogon zango da ƙasar ta yi a karo na uku a cikin watan jiya.

Sabon daftarin ,ya tanadi rufe hanyoyin kuɗaɗen da Koriya ta ke samu da kuma haramta shigar da wasu kayayaki a ƙasar.Ƙudirin ya sami amincewar manbobin kwamitin ƙasashe guda15, bayan da aka kwashe makonnin uku ana tattaunawa tsakanin China da Amurka.Koriya ta arewa ta yi barazanar kaiwa Amurka harin makamai nukiliya, inda har ba ta fasa yin wani atusayen sojin ba, na hadin gwiwa da Koriya ta kudu da aka shirya yi a makon gobe.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe