1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za ta fara shirin tsige Shugaba Trump

Abdul-raheem Hassan
December 18, 2019

Shugaba Donald Trump ya zargi jam'iyyar Demokrat da yunkurin juyin mulki, amma majalisar na zargin Trump da laifukan tilasta kasar Ukraine yin abinda ba ta yi niyya ba kan harkokin zabe da bijirewa binciken majalisa.

https://p.dw.com/p/3Uzp1
US-Präsident Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/B. Smialowski

Shugaba Donald Trump ya ce yunkurin tsigeshi da majalisar dokoki ke shirin yi wani shiri ne na juyin mulki.

"Tarihi ba zai taba yafewa ba" a cewar Shugaba Trump cikin wata doguwar wasika mai shafi 6 da ya aikewa kakakin majalisar Nancy Pelosi.

Za a kwashe kusan sa'o'i shida ana tafka muhawara kan batutuwa biyu da ya tada zancen tsigewawar, sannan rinjaye mafi karanci ne zai tabbatar da tasirin yunkurin tsige Shugaba Trump kafin zuwa mataki na gaba.