1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri: 'Yan bindiga sun kashe mutane

February 10, 2020

Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun hallaka mutane kimanin 30 tare da yin awon gaba da mata da kananan yara a kauyen Auno da ke kusa da birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3XYYe
Nigeria Boko Haram - Kinder als Selbstmordattentäter
Hoto: picture-alliancce/AP Photo/S. Maikatanga

A lokacin da suka kai hari a daren jiya Lahadi, 'yan bindigar sun kona motoci 18 tare da kwasar kayan abinci daga shaguna da su ka fasa. Yawancin wadan da harin ya rutsa da su matafiya ne da rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da jami’an tsaro su ka yi ta shafa.

Tuni dai gwamnan jihar ta Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da faruwar lamarin a hirarsa da manema labarai ciki har da wakilin DW Al-Amin Suleiman Muhammad inda gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa da rashin cikakken tsaro a kauyen na Auno.