Maiduguri: Harin bam ya kashe mutane 28 | Labarai | DW | 16.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maiduguri: Harin bam ya kashe mutane 28

Rahotannin daga Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno da ke a yanki arewa maso gabashin Najeriya na cewar wasu mata guda uku sun kai hare-haren kunar bakin wake a garin Mandarari da ke kusa da Maiduguri.

Masu aiko da rahotanin sun ce wasu da cikin matan sun tayar da jigidar bama-baman da ke a jikinsu daf da bakin wani sansani 'yan gudun hijira wanda hakan ya janyo mutuwar mutane 28 kana wasu 82 suka jikkata. Tun da farko daya daga cikin 'yan kunar bakin waken ta tayar da bam din da ke a jikinta da misalin karfe shida na yamma a cikin kasuwar sayer da raguna  a sa'ilin da jama'a ke haramar komawa gida.