Mai dakin shugaba Obama na ziyara a Afirka | Labarai | DW | 27.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mai dakin shugaba Obama na ziyara a Afirka

Cikin manyan batutuwa da ziyarar ta kunsa na zama yadda za a tunkari matsalolin da mata ke fiskanta a fannin ilimi tun bayan annobar Ebola.

USA, Nowruz im Weißen Haus

Michelle Obama

Uwargidan shugaba Obama na Amirka Michelle Obama ta sauka a nahiyar Afirka a ranar Litinin din nan tare da 'ya'yanta da mahaifiyarta a ziyarar da ke zama ta karfafa gwiwar yara mata dan su sami ilimi inda ziyarar ta fara da kasar da ta sha fama da annobar cutar Ebola.

Misis Obma dai ta samu tarba ta musamman a babban birnin kasar Laberiya, nan gaba kuma ta kama hanya zuwa Moroko kafin daga bisani zuwa kasar Spain.

A Laberiya bayan ganawa da Shugaba Ellen Johnson Sirleaf, mai dakin shugaba Obama za ta kuma ziyarci sansanin wasu yara mata da ke a garin Kakata inda cikin batutuwa da za a tattauna yayin taron za a ji yadda za a tunkari kalubalen da ke hana yara mata zuwa makaranta bayan da kasar ta sha fama da annobar Ebola wacce ta halaka mutane sama da 4800 a kasar.