Mahukuntan Najeriya na sake ɗammarar inganta tsaro | Siyasa | DW | 13.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahukuntan Najeriya na sake ɗammarar inganta tsaro

Najeriya ta ce tana shirin sayo karin jiragen sama da ma motoci na zamani da nufin shawo kan matsalar dake barazanar yamutsa al'amura a sassa daban-daban na kasar.

A cigaba da kokarin neman mafita a cikin rigingimun rashin tsaron da ake ta'allakawa da kwararar bakin haure, tarrayar Najeriya ta ce tana shirin sayo kari na jiragen sama da ma motoci na zamani da nufin shawo kan matsalar da ke barazanar yamutsa al'amura a sassa daban-daban na kasar.

Kama daga Jihar Benue inda da kyar da gumin goshi gwamnan ya kai ga tsallake rijiya daga baya, ya zuwa Jihar Katsinan da ma 'yan uwanta a Kaduna da Zamfara, dake fama da gungu na yan fashin shanu da dukiya, da ma uwa uba yankin Arewa maso Gabashin tarrayar Najeriya da ya tara baki da yan gari da sunan gwagwarmaya ta jihadi dai, sannu a hankali tarrayar Najeriya na karba ba dadi, sakamakon karin rigingimun rashin tsaron da suka kai ga wuyan sarakuna dama talakawa a kasar.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria Fernsehansprache ARCHIV

Shugaba Goodluck Jonathan

Gaza tasirin karfi na hatsi a bangaren mahukunta game kuma da dabarun diplomasiyasar kasar ta Najeriya dai tuni ya fara tada hankulan masu ruwa da tsakin dake kallon rikicin a matsayin babbar barazanar dake iya kawon cikas ga zabukan kasar na badi dama kila makomarta anan gaba.

Karancin hanyoyin samun mafita

Tuni dai dattawa a kasar suka fara karatun neman mafita a cikin jerin rigingimun da a fadar Dr Shattima Mustapha dake zaman tsohon ministan tsaron kasar ta Najeriya ke nuna alamu na gazawa a bangaren gwamnatin da ba ta kasa katabus duk da jerin na matakai da ma kasafin kudi mafi girma cikin kusan shekaru 40 a kasar.

“Abubawan nan kamar wai a nunawa gwamnatin ko an fi karfin ta ne. Alal misali a daukacin shekara ta 2013 bamu taba jin wani bam ko bindiga ko wani abu ya tashi a Maiduguri ba, sai da aka fara gangami na siyasa sai aka ce bam ya tashi a offishin gidan waya na Maiduguri. A bayan wannan bam ana nan ana ta surutu da maganganu da musayar yawu, masu wannan ta'asan suna nan suna da karfi sai suka fara kai hari kan garuruwa, yau a Kawuri gobe Konduga da Bama da Izge.”

Kalubalen tsaron na karuwa kullun

Kama daga Fulanin dake cin karensu babu babbaka a tsakiyar tarrayar Najeriya ya zuwa barayin shannun da suka addabi sashen Arewa maso Yamma da ma Larabawan dake taka rawa a cikin yakin ta'addancin kasar ta Najeriya kusan tsakiyar rigingimun na zaman baki na waje, abun kuma da ake ta'allakawa da rashin isassun kayan aiki dama rashin kulawar jami'an shigi da ficin dake da aikin tabbatar da kare iyakokin kasar daga bako na haram.

To sai dai kuma a cewar Comrade Abba Moro dake zaman ministan tsaron cikin gidan kasar ta Najeriya dai gwamnatin na matukar taka rawa da nufin kawo karshen matsalar da ta kalli shigar yan gwagwarmaya da makamai daga sassa daban daban na duniya.

Nigerien Maiduguri Autobombe Doppelanschlag März 2014

Wurin da tagwayen bama-bamai suka fashe a Maiduguri

“Muna tsakiyar shirin sayo motoci na zamani da nufin sintiri a kan iyakokin mu, sannan kuma muna kokarin shigo da fasahar da za ta bamu damar iya shawagi na iyakar mu tun daga sama. Na karshe kuma mafi muhimmanci na zaman kokarin na sayo karin jiragen da zasu taimaka mana shawagi a iyakokin mu. In kun sani hukumar mu ta shigi da fici na da jirage har uku biyu na aiki daya na kwance, muna magana da kamfanin Dornier dake mana gyara domin tada na ukun, bayan nan kuma muna kokarin sayen karin wasu jiragen har uku na shawagin iyakokin mu. Muna da imanin cewar da waddanan hanyoyi uku, hukumar shigi da ficin mu za ta shawo kan matsalar bakin hauren dake zaman annoba a garemu”.

Kasar ta Najeriya dai na da tsawon kilomita 1690 tsakaninta da kamaru a gabas, sannan da kilomita 1497 ta Arewa da jamhuriyar Nijer.

Tsawon kilomta 87 ne dai ya hada kasar ta najeriya da jamhuriyar chad ta arewa maso gabashin kasar da ya maida ita kasa mafi girma na iyaka a kudu da hanadar sahara.

Sauti da bidiyo akan labarin