Mahukuntan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na neman shawo kan rikici | Labarai | DW | 26.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahukuntan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na neman shawo kan rikici

Sabon firaministan kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ce gwamnati za ta ba da fifiko kan magance rikici

A wannan Lahadi sabon Firaminstan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Andre Nzapayeke, ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen mayar da doka da oda tare da kawo karshen rikici musamman na addinin tsakanin Musulmai da Kiristoci.

Sabon firamnistan tsohon jami'in Bankin raya kasashen Afirka, yana magana kwana guda bayan nada shi kan mukamun da sabuwar Shugabar gwamnatin wucin gadi ta Catherine Samba-Panza ta yi, wadda ita kanta kwanaki hudu ta shafe kan madafun iko bayan rantsar da ita.

Nzapayeke ya bayyana kalaman a cikin hira da kafofin yada labarai na Faransa. Kuma nan gaba kadan ake sa ran zai bayyana majalisar gudanarwa ta ministoci, wadanda za su yi aiki tare damin magance rikicin da kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fuskanta.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh