Mahmud Abbas ya yi kira da a dakatar da harba rokoki cikin Isra´ila | Labarai | DW | 25.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahmud Abbas ya yi kira da a dakatar da harba rokoki cikin Isra´ila

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yayi kira da a kawo karshen harba rokoki kana kuma a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra´ila bayan da sojoji Bani Yahudu sun cafke manyan jami´an Hamas su 33, a wani mataki na murkushe kungiyar ta masu kishin Islama. Shugaba Abbas ya nuna haka a ganawar da yayi da babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana. A wani samame da ta kai da asubahi a yankin Yamacin Kogin Jordan Isra´ila ta kame manyan ´ya´yan Hamas. Ministan Ilimin Falasdinawa Nassereddin al-Shaer da ´ya´yan majalisar dokoki msu 3 da kuma magadan garuruwa guda 4 na daga cikin wadanda aka kame. Da farko an jikata akalla Falasdinawa 4 a wani hari ta sama da Isra´ila ta kai a wani gidan ´yan Hamas da ke birnin Gaza. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce mutanen sun zo wucewa ne sannan harin ya yi kaca-kaca da ginin na sojojin sa kan Hamas tare da wasu gine gine dake kusa.