1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashi tamanin cikin dari na Jamusawa na mutunta lokaci

March 11, 2020

Sabanin kasashen Afirka, riko da lokaci na zama wani babban al’amari da Jamusawa suka yi amanna da shi wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum a wani lamari da ya samo asali shekaru aru-aru.

https://p.dw.com/p/3Z9Iz

Sabanin kasashen Afirka, riko da lokaci na zama wani babban al’amari da Jamusawa suka yi amanna da shi wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, hakan ya samo asali ne tun shekaru aru-aru wanda ya sa ake kiyasta cewa kashi tamanin da biyar cikin dari na Jamusawa ne ke mutunta lokaci. Mutunta lokaci shine gudanar da wani al’amari yadda aka tsara shi tare da aiwatar da shi kan wa’adin da aka kebe domin sa, daidakun al’umma da ma mahukunta a kasar Jamus kan tafiyar da al’amurransu ne bisa lokaci kama tun daga lokuttan aiki, kasuwanci dama na zurga-zurga. 


Wani abun da ke alamta hakan shi ne yin amfani da lokacin a bangaren sufurin ababen hawa na haya da suka hada da safa-safa da kuma kananan jirage da ke zurga-zurgar cikin gari da ma tsakanin gari da gari dukkaninsu an dorasu ne kan lokaci. Lamarin da ake ganin ya kamata kasashe masu tasowa irin namu na Afrika sun dabi’antu dasu, Ibrahim Baba Shatambaya malami a sashen nazarin kimiyar siyasa a jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakwato ya fayyace mana muhimmancin lokaci ga bil adama.


Sai dai labara ya sha banban a kasashe masu tasowa ida a lokutta da dama ake wofintar da alfanun da lokacin yake da shi inda har wani lakabi ake danganta saba lokaci da shi wai ‘Afrikan time’. Harwa yau Ibrahim Baba Shatambaya ya alakanta saba alkawali a kasashe masu tasowa da zama daya daga cikin sabubban koma bayan yankin yana mai cewa. Jamusawa dai na da ra’ayin cewa da a aje lokaci da kai ka yi latin minti guda gwamma ka kasance mintuna 5 kamin lokacin. hasali ma tana kai a ci tara ta kudi saboda bai mutunta lokacin da aka yi alkawari za hallara ba a kotu ga misali, yayin da asibita ma, likita zai ki ba shi kulawa matikar ya saba lokaci.