Mata na gujewa zuwa asibiti saboda corona
June 12, 2020Annobar coronavirus dai ta shafi al'ammura na yau da kullum tare da yin barazana ga mafi yawan harkokinmu na duniya, ka zalika a gefe guda cutar a halin yanzu ta yi fintakau da ta sanya ba a fiye mayar da hankali kan matsalolin kiwon lafiya da a baya ake fadin tashin ganin an yi yaki da su. To a bangaren mata masu juna biyu ma dai hakan take kan batun zuwa awon ciki, ko mata a halin yanzu suna zuwa awon ciki? wadanne ka'idoji aka tanadar ga matan na kare su daga kamuwa da cutar idan suka je asibiti yin awo kasancewar a mafiya asibitoci akan yi awo ne ga matan a rana guda? Masana kiwon lafiya dai na cewar cutar corona babbar barazana ce ga mata masu juna biyu kasancewar jikin mace na sauyawa a lokacin kuma tana fuskantar barazanar kamuwa da cutattuka a wannan lokacin.