Mahimmancin gidajen radiyo ga ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahimmancin gidajen radiyo ga 'yan gudun hijira

A jihar Adamawa ‘yan gudun hijira sun bayyana gamsuwarsu kan tasirin gidajen Radiyo ga rayuwar da suka tsinci kansu

Al'ummar da dama ne dai rikicin Boko Haram ya rabasu da ‘yan uwansu, maza da mata hada da kananan yara, don haka wasu daga cikinsu da ke gudun hijira a Yola, ke ganin kafar sadarwar radiyo, musamman na ketere na taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu na halinda suke ciki. Kamar dai yadda daya daga cikin yan gudun hijran mai suna Steaven Kaja ke cewa.

Ya dai yi tsokacin ne ganin yadda duniya ke ranar tunawa da mahimmancin gidajen radiyo.

Matasa musamman da mata suma sun bayyana yadda radiyon ke da tasiri a rayuwarsu, ga me da yadda suke daukan darusa dama moriya da suke samu daga kafafen radiyo.

Jama'a da dama dai na ganin radiyon na taka muhimmiyar rawa, na jan hankalin gwamnati da mahukunta, kan irin shawarwari da masanan harkokin tsaro ke bayarwa, musamman a yanzu ake fiskantar matsalolin yan ta'adda Najeriya da sauran wasu kasashen duniya. ta'addanci.

Sauti da bidiyo akan labarin