Najeriya: Martani kan umurnin harbe 'yan bindiga
August 19, 2019Ci gaba da ta'azarar wannan al’amari na kai hare-hare da kashe jama’a ba kakkautawa da ‘yan bindigar ke yi musamman kama daga yankuna Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna zuwa Jihar Katsina da ma wasu sauran sassan yanki arewacin Najeriyar ya kai ga shugaban kasar bai wa sojojin wannan umurni. Inda ya ce duk inda aka ga ‘yan bindigar da ke ta’annati ga rayuwar jama’a, to a kawar da su kawai bisa umurni na harbe su da aka bai wa sojojin a ganawar da ya yi. Wannan shi ne mataki na baya-baya nan da shugaban ya dauka a kokarin da ya dade yana ikirarin dauka domin shawo kan matsalar. Lamarin da ya sanya mai da martani musamman daga kungiyoyi na farar hula a Najeriyar.
Daukan wannan mataki da gwamantin Najeriyar ta yi ya zo dai dai lokacin da ake zargin sojojin da wuce iyaka ba ga farar hula ba kadai har ma ga abokan aikinsu a fanin tsaro wato ‘yan sanda. Kodayake wannan matsala ta kai wa kowa a wuya da ke zama tamkar wutar daji da ke kara ruruwa. Sai dai wasu masana harkokin tsaro a Najeriyar na dora ayar tambaya a kan dacewar wannan mataki na Shugaba Buhari musamman a dai dai lokacin da wasu jihohin kasar suka fara sulhu da masu kai hare-haren.
Wannan matsala ta ‘yan bindiga da ke kai hare-hare baya ga yin raga-raga da batun yanayin zamankewar alummu dabam-dabam, ta kuma hana aikin noma a yankuna da dama musamman a Dogon Dawa da ma ke karamar hukumar Birnin Gwari da ma Jihar Katsina, abin da ke jefa tsoron mumunar illa da hakan zai yi.