1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan shawarwarin zauren taron kasa a Najeriya

August 14, 2014

Bayan tafka takadamma mai zafi, wakilan taron kasa a Najeriya sun amince da kundin rahoton shawarwarin da suka kwashe watani uku suna tattauanawa a kai.

https://p.dw.com/p/1CuzI
Delegierte in Abuja
Hoto: DW/U. Idris

Amincewa da rahoton shawarwarin da mahalartar taron na Najeriya suka yi cikin ruwan sanyi bayan tada jijiyar wuya da ma hasashen cewa zaman muhawara a kan taron zai iya kaiwa ga dambacewa a tsakanin wakilan Arewaci da Kudancin kasar, ya kasance lamari na ban mamaki ga mutane da dama, musamman jan dagar da wakilan Arewacin kasar suka yi, a kan gabatar da sabon tsarin mulki na 2014.

Sanin cewa batun zargin shigar da sabon tsarin mulki a rahoton taron ne ya sanya tada jijiyar wuya har da kurarrin da wakilan arewacin Najeriyar suka yi na janyewa daga taron, shin sauya sunan kundin daga tsarin mulki zuwa shawarari ya sanya sun gamsu kenan da daukacin rahoton da abinda ke cikinsa har suka kaiga amincewa da shi?

Miss Ankio Briggs wakilayar yankin kudancin Najeriya na Niger Delta ne wadanda suka fafata a tsakaninsu da takwarorinsu na arewacin kasar ko sun gamsu da sakamakon taron da suka nuna ja a kan batutuwa da dama?

‘'Ba zaka ce kana farin ciki da komai ba , to amma dai har zuwa wani mataki mun gamsu , domin mun zo nan ne don mu tattauna matsalolin da suka dade suna damun Najeriya, amma bisa la'akari da abubuwan da muka cimma a cikin watani hudu ina ganin mun yi aik sosai.

Abin jira a ganin shine yadda za'a aiwatar da rahoton saboda sanin shawarwari irin wadnan da aka gudanar a baya har yanzu suna nan suna shan kura, abinda ya sanya masharhanta kalon taron mai kama da na shan shayi ga wakilai sama da 400 da suka kwashe kusan watani uku suna tada jijiyar wuya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinado Abdu Waba