1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin boye halittun wasu duniyoyi a Amirka.

Gazali Abdou Tasawa
July 17, 2019

Wasu Amirkawa sama da miliyan daya na shirin kai mamaye a cibiyar sirri ta sojojin Amirka a Jihar Nevada inda suke zargin gwamnatin Amirka na boye halittun wasu duniyoyi da suka shigo wannan duniya tamu.

https://p.dw.com/p/3MBGN
USA Grenzzaun Area 51 in Nevada
Hoto: Getty Images/D. Callister

A daidai lokacin da ake bukukuwan cikar shekaru 50 da dan Adam ya sauka a duniyar wata, a kasar Amirka wasu mutane sama da miliyan daya sun sanar da shirin kai farmaki a wata cibiyar sojojin Amirka ta sirri da ke a jihar Nevada da aka fi sani da Area 51 inda suke zargin gwamnatin Amirka na boye wasu mutane ko kuma halittu na wasu duniyoyi na daban da ake yi wa lakabi da Alien. 

Mutanen kimanin miliyan daya da dubu 300 sun kaddamar da wani kampe a shafin sada zumunta na Facebook da suka yi wa lakabin Storm Area 51, inda suka tsaida ranar 20 ga watan Satumba mai zuwa a matsayin ranar da za su afka wa cibiyar sojojin ta sirri da ke a saharar Jihar ta Nevada wacce hatta Hukumar Leken Asiri ta Amirka ta CIA sai a shekara ta 2013 ta gano da akwai ta. 

Shekaru da dama kenan dai da wasu masana kimiyya ke binciken gano wasu halittun wasu duniyoyi da suke zargin sun shigo wannan duniya tamu ba tare da yin nasara, halittun da amma wasu Amirkawa ke zargin gwamnatin kasar tasu na boye su a wanann cibiyar sirri ta sojojin kasar da ke a jihar ta Nevada.