Mahawara akan makamai masu guba na Siriya. | Siyasa | DW | 25.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawara akan makamai masu guba na Siriya.

Ana ci gaba da nuna shakku da kuma yin tababa dangane da sanarwar da wani jami'in hukumar leƙen asirin Isra'ila ya bayyana cewar Siriya na yin amfani da makamai masu guba.

Shugaban hukumar leƙen asiri na ƙasar ta Isra'ila Janar Itai Brun shi ne ya bayyana cewar suna da shaidu na hotunan bidiyo da kuma gwaje gwaje da aka gudanar akan marasa lafiya da ke fama da cututuka da suka shafi nufashi, a garuruwan Homs da Hama.

Waɗanda suka shaƙi sinadarin makamin gubar Sarin a farmakin da sojojin gwamnatin suka kai a tsakiyar watan Maris da ya gabata.

Gwamnatin Isra'ila na da shakku akan Sriya dangane da yin amfani da makaman

A boy, affected in what the government said was a chemical weapons attack, is treated at a hospital in the Syrian city of Aleppo March 19, 2013. Syria's government and rebels accused each other of firing a rocket loaded with chemical agents outside the northern city of Aleppo on Tuesday, an attack which a cabinet minister said killed 16 people and wounded 86. REUTERS/George Ourfalian (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Marasa lafiya da suka shaƙi gubar a birnin Aleppo

Har yanzu dai fira ministan na Isra'ila Benyamen Netanyahu ya gaza tabbatar da gaskiyar labarin. Sannan Amurika ma wace tun da farko ta yi gargaɗin cewar idan Siriya ta kuskura ta yi amfani da makamai masu guban za ta gane cewar shayi ruwa ne, ita ma ya zuwa yanzu ba ta jiƙa ba ko kaɗan da sakamakon bincike da janar Brun ya sanar a wajan wani taron manema labarai kan harkokin tsaro a wannan mako.

Eyal Zisser wani malamanin jami'a ƙwarrare akan Siriya wanda ke koyar wa a jami'ar Moshe Dayan da ke a birnin Tel Aviv.Ya ce ba ya tsamanin Siriya ta yi amfani da makamai masu guba, sannan kuma ya bayyana ra'ayinsa dangane da matsayin da shugabannin Isra'ilan suka dage akan su na ƙin tabbatar da labari.

Ya ce : ''Ba shakka sun yi haka ne domin basu da wasu hujojin masu ƙwari ya ce kuma shugaban gwamnatin ya na sanne sarai da irin abinda kan iya biyo baya idan ya ƙarda labarin.''

A farkon shekarun 1970 ne ƙasar Siriya ta fara bunƙasa harkokin makamai masu guba tare da taimakon Rasha kafin daga bisani Iran ta riƙa tallafa mata. A cikin wasu cibiyoyinta guda hudu da suka haɗa da Allepo da Homs da kuma Hama waɗannan sune ciboyin da aka sanni.

Ƙasashen yammancin duniya na ci gaba da gudanar da bincike akan Siriya

PENZA REGION, RUSSIA. SEPTEMBER 15, 2005: Critical warfare processing warehouse in the chemical weapons storage and disposal facility in the Leonidovka village, where the head of the federal department of the safe storage and disposal of chemical weapons Valery Kapashin arrived with a visit.. Foto: Alexander Karelin +++(c) dpa - Report+++

Na'ura sarafa guba

Tun lokacin da aka fara yaƙin na Siriya ƙasashen duniya suke ƙokarin sannin abinda ke faruwa a cikin waɗannan man'yan kamfanoni da ke sarafa makaman, amma ba tare da samun nasara ba. Dina Esfandiry ƙawarrara ce a wata cibiyar da ke yin bincike a London. Ta ce shugaba Bashar Al Assad na iya yin amfani da makaman idan tura ta kai masa bango.

Ta ce : '' Ya danganta da yadda Shugaban Siriya zai fuskanci matsin lamba, inda har ya ga ba shi da zaɓi ya kasance cikin wani hali ne na ko a yi rai, ko a mutu, to kam zai iya yin amfani da makaman na ƙare dangi.''

Ya zuwa yanzu dai man'yan ƙasashen duniya na saka ido so sai akan Siriya domin sannin irin matakan da zasu dauka ko da hakan ya tabbata.

Daga ƙasa za a iya sauraran wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin