Mahawara a Najeriya a kan rajistan baƙi | Siyasa | DW | 03.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawara a Najeriya a kan rajistan baƙi

Majalisar dattawa Najeriya na tattauna batun dokar yin rajista na baƙi 'yan ci rani daga yankin arewa zuwa kudu da gwamnatin jihar Imo ta ƙaddamar.

Wannan Tattaunawa ta majalisar dattawan na zuwa ne daf da lokacin da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a Jihar Enugu suka ƙaddamar da wani tsari na rajistar tantance baƙi masu zuwa ci rani Jihar daga sassa daban-daban na Najeriya,musamman daga yankin arewaci. Masu zuwa ci ranin dai a jihar kowane na ba da Naira dubu ɗaya domin samun rajistan, abin da wasu ke kallon cewar ya saɓama doka.

Tsarin ya janyo tsokaci jama'a da dama waɗanda ke ganin ya saɓama doka

Ausländer Verhaftungen in Kano Nigeria

Baƙi ' yan ci rani a Najeriya

Manazarta da ƙwararru kan shari'a na ganin cewar tsarin na yi wa baƙi rajista galibi 'yan arewacin Najeriya tsari ne da ya keta dokar ƙasar ta zamantakewa da yanci. A baya-bayan nan Rundunar Soji ta Enugu ta kame wasu ɗaruruwan 'yan asalin arewacin na Najeriya da ke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Rivers ci rani, tare da zargin cewar sun shigo yankin kudancin da nufin tada hankula inda aka ci gaba da tsare wasu yayin da wasu kuma aka sakesu.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton a kan tattaunwar 'yan majalisar Dattawa na Najeriyar da kuma rahoton da wakilinmu na Lagos Masur Bala Bello ya aiko mana a kan farautar baƙi da jami'an tsaro ke yi

Mawallafi : Muhammad Bello
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin