Mahaukaciyar guguwar nan ta Sandy na ci-gaba da ɓarna a Amirka | Labarai | DW | 30.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaukaciyar guguwar nan ta Sandy na ci-gaba da ɓarna a Amirka

Yankunan ƙasar Amirka na yawan fuskantar miyagun iska masu ƙarfi wanda ke haddasa asarar rayukan jama'a.

A kalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon bugawar mahaukaciyar guguwar nan da a kawa lakabi da sunan Sandy a Amirka. Wadanda suka mutun sun hada ne da 12 a yankin New York yayin da 1 ya riga mu gidan gaskiya a kasar Canada inda guguwar mai karfin gaske ta kada a jiya Littanin da yamma. Tun can farko dai hukumomin yankunan New York sun ce sun dauki kwararan matakai na ganin an rage barnar da iskan za shi yi. Hukumomin agaji sun bayana cewar akasarin wadanda suka hadu da ajalin nasu ya biyo bayan faduwar itace ne ko kuma motocin da ke fada musu bisa ga karfin iskan. Yanzu haka kimanin jirage dubu 11 ne aka hanawa tashi a kasar ta Amirka a wani matakin rigakafi. Makamanciyar wannan guguwar mai sunan katarina da ta buga a 2005 ta haifar da ce-ce-ku-ce a lokacin ikon George Bush da jama'a suka zarga da rashin tanadin matakai.

Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita : Umaru Aliyu