Mutum akalla 23 aka tabbatar sun mutu a sakamakon wata mahaukaciyar guguwa da ta tafka barna a jihohin Mississippi da Alabama da ke kudancin Amurka.
Wata mahaukaciyar guguwar iska mai tafe da ruwan sama mai karfin gaske ce, ta lakume rayuka akalla ashirin da uku tare da lalata tarin gine-gine da katse hanyoyin wutar lantarki, a jihohin Mississippi da Alabama da ke kudancin Amurka.
Yanayin munin lamarin ya sa, hukumomi sun gargadi jama'a da su yi taka tsan-tsan a yayin da suke cewa, har yanzu akwai kalubalen da ake fuskanta mai barazana ga rayuwar al'umma a yankunan. Iftila'in ya tafka barna da kawo yanzu ba a iya tantance asarar da aka tafka daga guguwar iskar ta daren ranar Jumma'ar da ta gabata ba.