1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mai fama da damuwa ya kai hari a jirgin kasa a Jamus

Ramatu Garba Baba SB
November 7, 2021

Hukumomin Jamus na ci gaba da bincike inda suka ce wanda ya kai hari kan jama'a da wuka a cikin jirgin kasa yana fama da tabin hankali.

https://p.dw.com/p/42hIL
Deutschland Messerangriff im ICE zwischen Regensburg und Nürnberg
Hoto: Ayhan Uyanik/REUTERS

Mahukunta a Jamus sun gano maharin da ya daba wa fasinjoji wuka a cikin jirgin kasa, ya nuna alamun tabin hankali kuma harin ba shi da nasaba da aiyukan ta'addanci. Jami'an 'yan sanda da wadanda suka gudanar da binciken ne suka fada ma manema labarai a wannan Lahadin, sai dai sun ce ba a kai ga tantance dalilansa na kai harin na kan uwa da wabi ba.

Karin bayanin da suka yi, shi ne na cewa, mutumin dan shekaru 27 da haihuwa ne, kuma dan asalin kasar Siriya ne da ya shigo Jamus tun a shekarar 2014 ya kuma rasa aikinsa kwana guda kafin kai harin.

A wannan Asabar da ta gabata mutumin dauke da wuka mai tsayin mita uku, ya far ma fasinjojin inda ya kama daba wa duk wanda ke kusa da shi wuka, daga bisani ya tsere zuwa wani taragon jirgin inda nan ma ya dabawa wani mutum guda wuka. Biyu daga cikin mutanen hudu na kwance a gadon asibiti.