1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe sojin Najeriya 30

Abdul-raheem Hassan
July 3, 2022

Wani jami'in soja da ke fagen daga a yankin Shiroro na jihar Niger, ya ce “Abin takaici ne mutuwar sojojin da ke yunkurin ceto fararen hula da aka yi garkuwa da su, amma duk da haka ba za su ja da baya ba."

https://p.dw.com/p/4DZkG
Sojan Najeriya a yankin Bama da ke arewa maso gabashin NajeriyaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP

Rahotanni majiyoyin tsaro a Najeriya, na cewa akalla sojojin kasar 30 sun mutu a wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga su ka yi musu a yankin Shiroro na jihar Neja a farkon mako mai karewa.

Sojojin na cikin jami'an tsaron da aka tura domin neman ma'aikatan hakar ma'adinai da aka sace a ranar Laraba, ciki har da 'yan kasar China hudu.

Babu tabbacin kungiyar da ta kai wannan mumunar hari a kauyen Ajata Aboki da ke jihar Niger a arewa maso yammacin Najeriya, sai dai Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya Asabar cewa " ‘yan bindigar ‘yan bakin ciki ne, kuma za su fuakanci hukunci. Mazauna Shiroro za su ga adalci."