Mahamadou Issoufou ya kai ziyara a birnin Gao na arewacin Mali | Labarai | DW | 06.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahamadou Issoufou ya kai ziyara a birnin Gao na arewacin Mali

Shugaban Jamhuriyar Nijar ya yaba da nasarorin da AFISMA ta samu a yakin da ta kaddamar domin belin yankin arewacin kasar Mali.

epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++

Mahamadou Issoufou

Alhaji Mahamadou Issoufou, wanda a wannan Lahadi ke cika shekaru biyu kan karagar mulki, ya ziyarci sojojin Nijar da aka tura a birnin Gao na arewacin kasar Mali, a karkashin rundunar AFISMA.A jawabin da ya gabatar, shugaban ya kara karfin gwiwa ga dakarun kasa da kasa,domin su kara matsa kaimi wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda da suka mamaye yankin arewacin Mali.

Mahamadou Issoufou ya ce lalle an samu nasarori a wannan yaki, to amma har yanzu da sauran rina kaba.Tun lokacin gamayyar kasa da kasa ta kaddamar da yaki da 'yan tawaye a arewacin Mali,Mahamadu Isufu shine shugaban kasar Afirka da ya ziyarci wannan yanki.Baki daya Nijar na da jimlar sojoji 675 a cikin rundunar AFISMA.

A wani labarin kuma da ya shafi Mali, wani dan sanda ya hallaka soja daya a birnin Bamako.

Wannan hadari ya abku a barikin 'yansanda ta GSM, a yayin da wata tawagar sojoji ta yi yunkurin karbar makamai daga rukunin 'yan sanda masu goya bayan sojojin da suka yi mulki a shekara da ta gabata.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi