Mahajjata na hawan Arfa | Labarai | DW | 11.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahajjata na hawan Arfa

A wannan Lahadin ce alhazai wanda yawansu ya haura miliyan guda da rabi su ke yin tsayuwar Arfa wanda ke nuni da cewar aikin Hajjin bana ya kai kololuwarsa.

Yayin wannan tsaiwa dai alhazan za su shafe wunin yau suna salloli da zikiri da addu'o'i. Tun a ranar Juma'ar da ta gabata ce wasu mahajjatan suka fara tafiya Muna domin yin tsayuwar Arfa din a yau. A bana ne dai aka cika shekara guda bayan da aka gamu da wani ibtila'i na rasuwar dubban Alhazai sakamakon wani turmutsutsu. Sai dai a wannan karo hukumomi a Saudiyya din sun ce sun dauki dukkanin matakan da suka kamata domin kauracewa matsalar da ta auku a bara wadda ita ce mafi muni da aka gani a tarihin aikin hajji na baya-bayan nan.