Mahajjata miliyan biyu ke hawan Arfa | Labarai | DW | 31.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahajjata miliyan biyu ke hawan Arfa

Mahajjata maza da mata sanye da fararen harami na addo'o da karatu Alkur'ani mai girma da nufin neman kusanci ga Allah.

Mekka Pilger auf dem Berg Arafat (REUTERS)

Mahajjata na hawan Arfa a Saudiya.

Wannan rana dai shi ke zama rana mafi mahimmaci a cikin ranakun ayyukan hajji ga musulmai da suka samu damar ziyartar kasa mai tsarki, wannan ya sa dubban Alhazai suka dukufa wajen mika kukan su ga madaukakin tsariki dan neman biyan bukatunsu. Wani mahajjaci daga Najeriya, ya yi addu'ar neman hadin kai da zaman lafiya.

"Na zo hajji, kuma na roko Allah ma daukakin tsarki da ya hada kan musulman duniya, ya kuma baiwa Najeriya da sauran kasashen duniya zaman lafiya."

Tarihi dai ya nuna cewa karni 14 da suka shude, Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi ya gabatar da huduba ga musulmai a wannan wuri. Hukumomin kasar Saudiya sun tsaurara matakan tsaro da ma'aikatan jinya dan baiwa mahajjata damar gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali dan kaucewa tirmitsitsi da zai cutar da al'umma.