Magungunan Aids ko Sida sun yi karanci a Najeriya | Zamantakewa | DW | 01.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Magungunan Aids ko Sida sun yi karanci a Najeriya

Kimanin masu dauke da kwayar cutar HIV/ Aids ko Sida kusan miliyan uku a Najeriya ba sa samun magunguna da ke rage radadin cutar, a cewar masana harkokin lafiya.

Saurari sauti 03:28

Rahoto kan halin da masu fama da Aids ko Sida ke ciki a Najeriya

Alkaluman da masana suka bayar sun nunar da cewa daga cikin mutane 3 400 000 da aka gano su na dauke da HIV a Najeriya, kimanin mutane 8 900 000 ne ba sa samun magungnan saboda raguwar tallafi da kungiyoyin agaji da kuma kasa da kasa ke bayarwa domin yaki da cutar.

Absolon Habila shugaban Kungiyar masu dauke da Aids ko Sida a jihar Gombe ya tabbatar da matsala ta karancin magungunan a wasu jihohi, lamari da ke barazana ga kokarin da hukumomi ke yi na dakile yaduwar cutar da ke hallaka dubban mutane. ya ce in hukumomi ba su dauki matakai da suka da ce ba, to aikin da aka yi na yaki da cutar da nasarorin da aka samu za su lalace.


Sai dai hukumomin da ke yaki da cutar sun tabbatar da cewa ba ko ina ne ake da karancin magungunan ba kamar yadda Hajiya Fatima Mai Samari jamia a hukumar yaki da cutar Sida ta jihar Gombe ta shaida wa DW.

Masana da masharhanta sun nemi gwamnatoci a dukkanin matakai a Najeriya da su gaggauta samar da kudaden tallafi na bincike da gwaje-gwajen gami da magunguna da abinci ga masu dauke da Aids ko Sida musamman a wuraren da aka fara samun karancin magunguna.


Sauti da bidiyo akan labarin