Magoya bayan tsohon shugaban Cote d′ivoire sun yi zanga zanga | Labarai | DW | 16.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Magoya bayan tsohon shugaban Cote d'ivoire sun yi zanga zanga

'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye, domin tarwatsa magoya bayan tsohon Shugaban Cote d'Ivoire Gbagbo.

'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye, domin tarwatsa masu zanga zangar da ke goyon bayan tsohon Shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo a birnin Abidjan.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ruwaito cewa, kimanin matasa 50 wadanda ke zanga zangar neman sakin tsohon Shugaba Gbagbo, sun yi yunkurin tsallaken shingen 'yan sanda, abun da ya janyo martani ta wajen watsa hayaki mai saka hawaye.

Laurent Gbagbo ya mulki kasar ta Cote d'Ivoire da ke yankin yammacin Afirka daga shekara ta 2000 zuwa shekara ta 2011. Shugaba Alassane Ouattara ya kawar da shi a zaben watan Disamba na shekara ta 2010, amma Gbagbo yaki amincewa da shan kayi na zaben, wanda ya janyo rikici kafin kawar da shi daga madafun iko, a watan Afrilu na shekara ta 2011. Kuma yanzu haka Gbagbo na fuskantar tuhuma a kotun duniya da ke birnin Hague. Kimanin mutane 3000 sun hallaka cikin rikicin da ya biyo bayan zaben.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas