Magance shigar bakin haure zuwa Turai daga Nijar | Siyasa | DW | 10.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Magance shigar bakin haure zuwa Turai daga Nijar

Kungiyoyin fararen hula da na matasa a Nijar sun kaddamar da wani shiri da ke nuna illar shiga Turai ta barauniyar hanya wanda a yanzu haka ya zama ruwan dare.

Kungiyoyin dai na amfani da wadanda suka shiga Turai ta barauniyar hanya wajen bayyana irin hadarin da ke tattare da wannan harka. A kan haka ne ma suka nuna wani faifan bidiyon na mintoci akalla 45 da ke kumashe da bayanai kan wannan batu.

Überfahrt Mittelmeer Opfer von Schiffsunglücken Flash-Galerie

Lodin fasinjoji fiye da kima a jiragn ruwa kan jawo kifewar jirgin da ke dauke da bakin haure a tsakiyar teku.

Matasan da kungiyoyin suka ce wannan dabara da suka dauka ta amfani da bidiyon zai taimaka wajen kawar da duk sha'awar da ke da wasu ke da ita ta shiga Turai ta hanyar da aka haramta musamman kana suna amfani da wannan tsari ne don nunawa jama'a cewar shiga Turai fa daidai ya ke da abin nan da ake cewa ''hange dala ba shi ne shiga birni ba''.

Da ya ke tsokaci kan wannan batu, Malam Kabirou Oumarou shugaban kungiyar matasan Nijer da ke kira AJS cewa ya yi sun dau wannan kafe din ne don su nunawa matasa hakikanin bainda ke tattare da wannan bukata da mutane ke da ita ta shiga Turai.

Toter Soldat in Mangaizé

Yunwa da kishirwa da zafi a sahara kan jawo rasuwar bakin hauren da ke kokarin shiga Turai.Shi kuwa shugaban kungiyar farar hular nan ta CODDAE Alhaji Mustapah Kadi ya ce su a nasu bangaren kira suke ga matasa da ke son zuwa Turai da su tafi da takardu na gari su kuma nemi izinin shiga Turai din ta hanyoyin da hukuma ta shardanta inda za su kasance suna zaune kasashen da izinin hukuma maimakon su kansance suna zaune ba bisa ka'ida ba wanda hakan zai sanya su gaza samun aiki na kirki da sukunin yin walwala kamar koma.

Wannan shirin na kungiyoyin fararen hular da na matasan na zuwa ne a yayin da ake cigaba da samun macewar bakin haure a teku da hamadar saharar Nijar a kokarin da suke na shiga Turai ta kowanne hali, lamarin da kasashen da wannanbatu ya shafa da kungiyar tarayyar Turai ta EU ke ta fadi tashi wajen ganin an kawo karshensa.

Sauti da bidiyo akan labarin