1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance rikicin Sudan ta Kudu

January 1, 2014

Fada na kara zafafa yayin da ake shirin fara tattaunawa domin magance rikicin da kasar Sudan ta Kudu ke fuskanta

https://p.dw.com/p/1Ak0B
Hoto: Reuters

Masu shiga tsakani na kasashen Afirka sun ce ana shirin gudanar da tattaunawar sulhu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, tsakanin bangarorin da ke rikici a kasar Sudan ta Kudu.

Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar sun zabi wakilai da za su wakilce su yayin taron na tattaunawa. A wannan Talata da ta gabata, wa'adin da shugabannin kasashen gabashin Afirka suka diba wa sassan wa'adin na hawa kan teburin sulhu. Wani lokaci a wannan Laraba wakilan ke isa birnin na Addis Ababa.

Kuma har yanzu ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula duk da shirin fara tattaunawar. Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun 'yan tawaye masu biyayya wa Riek Machar sun kwace garin Bor helkwatar Jihar Jonglei daga hannu dakarun gwamnati.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane dubu daya sun hallaka tun lokacin da rikicin ya barke, lokacin da Shugaba Kiir ya zarge tsohon mataimakinsa Machar da yunkurin kifar da gwamnati.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu