1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magajiyar Merkel ba za ta nemi shugabanci ba

Mouhamadou Awal Balarabe
February 10, 2020

Shugabar jam'iyyar CDU da ke cikin kawancen mulkin Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta bayyana aniyar sauka daga mukaminta tare da dakatar da yunkurinta na tsayawa takarar shugabancin gwamnati a zabe mai zuwa.

https://p.dw.com/p/3XZ9s
Kanzlerin Merkel und AKK Mimik
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Soeder

Watanni goma sha hudu Annegret Kramp-Karrenbauer ta yi a kujerar shugabancin jam'iyyar CDU, amma yanayin siyasar da Jamus ta samu kanta a ciki ya sa ta samu kanta a halin gaba kura baya siyaki. Hasali ma dai, an yi mata kallon wacce za ta gaji Angela Merkel a matsayin shugabar gwamnati bayan ta kammala wa’adinta na hudu kuma na karshe a shekara ta 2021.

Deutschland Berlin | PK Klimakabinett nach Marathonsitzung | Angela Merkel u.a.
Hoto: Getty Images/AFP/A. Schmidt

Domin tabbatar da cewa ta dada fahimtar makamar aiki ne ya sa Merkel nada wacce ake wa lakabi da "AKK" a mukamin ministar tsaron Jamus. Sai dai kuma abokan hamayyarta sun zargeta da gaza gudanar da aikinta yadda ya kamata. Sai dai rikicin siyasa a jihar Thuringia ya zamewa Kramp-Karrenbauer kadangaren bakin tulu sakamakon hada gwiwa da jam'iyyarta ta CDU ta yi da AfD da ke kyamar baki wajen zaben gwamnan jihar, lamarin da ya sa ta ya da kwallo domin ta rabu da kuda

Babban abin da aka fi zargin Annegret Kramp-Karrenbauer shi ne rashin karfin fada a ji, lamarin da ya sa 'ya'yan jam'iyyar CDU na jihar Thuringia suka yi gaban kansu wajen zaben dan takarar da ba su da dangantaka da shi tare da yin watsi da umurnin da ta bayar. Ta yi niyyar dorawa inda uwar dakinta Angela Merkel ta tsaya sai dai rashin hada kawunan 'ya'yan jam'iyyarta ta CDU ya sa ta yi murabus. Elmar Brok, memba na kwamitin koli na CDU ya nuna bakin ciki game da murabus din AKK

Berlin | Annegret Kramp-Karrenbauer und Angela Merkel
Annegret Kramp-Karrenbauer da Angela MerkeHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

"Ina ganin murabus dinta bai dace a wannan lokacin ba, wannan ne ya sa shiga cikin mummunan yanayi."

Amma bayan mummunan koma baya da ta samu a zaben majalisar Turai da kuma a wasu zabbukan jihohi a shekarar 2019, AKK ta yi ta furta wasu kalamai da suka kaita suka baro. Annegret Kramp-Karrenbauer, uwar ‘ya’ya uku, ta soki 'yancin fadan albarkacin baki a yanar gizo bayan wani mai aika sako ta Youtube ya soki manufofin gwamnatin Jamus. Sannan kuma shawarta ta samar da wani yanki na tsaro na kasa da kasa a arewacin Siriya ba tare da tuntubar abokan aikinta ministan harkokin waje ba, da kuma kawanyenta na NATO, ya zubar mata da mutunci a idanun kasa da kasa.