1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafitar rikicin Musulmi da Kirista a Tsakiyar Afirka

July 12, 2017

A cewar shugabanin addinan biyu da suka jagoranci wannan taro a Kamaru suna da buri ne na ganin an samar da kyakkyawan yanayi da dukkanin bangarorin addinin biyu za su rika zama da juna.

https://p.dw.com/p/2gOYr
Zentralafrikanische Republik Präsidentschaftswahl
Hoto: Reuters/S. Modola

A kasar Kamaru ana ci gaba da gudanar da taron kyautata huldar dangantaka tsakanin Kiristoci da Musulmi na kasashen yankin Tsakiyar Afirka. Taron wanda ya hada limaman Kiristoci mabiya darikar Katolika da na addinin Musulunci na da burin samar da zaman lafiya a kasashen yankin, inda rigingimu da dama ke rikidewa zuwa na addini.

A cewar shugabanin addinan biyu da suka jagoranci wannan taro suna da buri ne na ganin an samar da kyakkyawan yanayi da dukkanin bangarorin addinin biyu za su rika zama da juna  ba tare da wata tsangwama ba. Misali a Jamhuiriyar Afirka ta Tsakiya irin wannan rikici ya yi tsamari ta yadda al'ummar kasar Musulmi da Kirista ke ta faman zubar da jinin juna irin wannan taro a cewar mahalartan zai taimaka a wajen samar da fahimta tsakanin juna.

Shugabanin dai na son a ci gaba da cudanya da juna su ziyarci juna abin da ke zama darasi ga mabiyansu.