1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita game da sabani akan rikicin Sudan ta Kudu

January 22, 2014

Shugaban Sudan ta kudu ya bukaci yin sulhu da Majalisar Dinkin Duniya duk da zargin da ya yi mata na nuna son kai a rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1Avn5
Konflikt im Südsudan Regierungssoldaten 02.01.2014
Hoto: Samir Bol/AFP/Getty Images

Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu ya bukaci sasantawa da Majalisar Dinkin Duniya duk kuwa da cewar a baya ya zargi majalisar da nuna goyon baya ga bangare guda a rikicin da ya barke a kasar a 'yan makonnin da suka gabata. Wata sanarwar da ta fito daga ofishin shugaba Salva Kiir a wannan Larabar (22.01.2014), ta ce a shirye yake ya bada cikakkiyar kariya da kuma mutunta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa. Sai dai kuma sanarwar ta kara da cewar, shugaban kasar yana ganin kamar tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a Sudan ta Kudun ta yi karan tsaye ga huruminsa. Hakanan sanarwar ta ce, majalisar ba ta yi Allah wadai da irin ta'asar da 'yan tawayen Sudan ta Kudu suka tafka a lokacin rigingimun kasar ba.

A halin da ake ciki kuma ministar kula da harkokin wajen Kenya Amina Mohamed, ta kare matakin da kasar Yuganda ta dauka na tura dakarunta zuwa Sudan ta Kudu, wanda ta bayyana da cewar, kungiyar ci gaban kasashen gabashin Afirka ta IGAD na yin marhabin dashi:

Ta ce "Kokarin bada kariya ga muhimman wurare irin su filin sauka da tashin jiragen sama a Sudan ta Kudu, abin marhabin lale ne ga kungiyar Ci gaban kasashen yankin gabashin Afirka domin kuwa matakin ne ya saukaka aikin samar da agaji ga mabukata a kasar, kuma in ba don hakan ba, to, kuwa da zai yi matukar wahala a kai agaji ga Sudan ta Kudun.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu