Maduro: Dole Guaido ya fuskanci shari'a
February 13, 2019Talla
A wata hira da wani gidan talabijin na kasar Lebanon, Maduro ya ce laifin da Guaido ya aikata na ayyana kansa a matsayin shugaban kasar na riko ya saba doka kuma hakan ka iya jawo rarrabuwar kai tare da janyo wasu kasashen ketare ciki har da Amirka su afkawa kasar.
Wannan ne ma ya sanya shugaban cewar muddin wata kasa ta yi kuskuren shiga kasarsa to za ta dandana kudarta. Amirka da wasu kasashen Turai dai na goyon bayan Guaido kan batun kawar da Maduro daga mulki yayin da China da Rasha ke adawa da wannan mataki.