Madugun ′yan tawayen Mozambik ya fito fili | Labarai | DW | 04.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Madugun 'yan tawayen Mozambik ya fito fili

Madugun 'yan adawa na kasar Mozambik ya fito daga maboyarsa

Madugun 'yan tawayen kasar Mazambik Afonso Dhlakama ya fito daga maboyarsa zuwa Maputo babban birnin kasar, abin da ke tabbatar da shirin zaman lafiya wanda ya kawo karshen shekaru biyu na zaman tankiya da yuwuwar sake komawa yakin basasa.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ga lokacin da jirgin saman da ya dauko Dhlakama ya sauka, inda ya samu tarba daga jami'an diplomasiya, kuma nan gaba zuwa gobe Jumma'a zai gana da Shugaba Armando Guebuza, domin karfafa shirin zaman lafiya na kasar ta Mozambik. Ana sa ran Dhlakama zai yi takara a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman