Macron: Za mu yaki ta′addanci a Mali. | Labarai | DW | 19.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron: Za mu yaki ta'addanci a Mali.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci hadin kan kungiyar tarayyar Turai EU da kuma Jamus wajen yaki da 'yan Jihadi a Mali.

A ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jaddada kudirinsa na yaki da masu tsatsauran ra'ayi da ke ikrarin jihadi a Mali da kuma yankin Sahel.

Da yake jawabi tare da shugaban Mali Ibrahim Boubakar Kaita a taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a sansanin sojin na Gao dake arewacin Mali inda aka jibge sojoji 1600. Macron ya sha alwashin hada hannu da kungiyar tarayyar Turai da kuma Jamus domin cimma manufa ta murkushe kungiyoyin jihadi a yammacin Afirka. 

Tun dai a lokacin ykin neman zabensa Macron ya sha alwashin cewa zai baiwa yaki da ta'addanci fifiko, bayan wasu hare hare da aka kai a Faransa a shekarar 2015 sun hallaka mutane fiye da 230.

Galibin kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi da Faransa ke gwagwarmaya da su dai suna da alaka da kungiyar al-Qa'ida reshen arewacin Afrika.