1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hada kai da Afirka a batun bakin haure

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 4, 2018

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen Afirka da na Turai da su hada hannu waje guda domin samo mafita a kan matsalar bakin haure da ke kwarar nahiyar Turan.

https://p.dw.com/p/30qfN
Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel MacronHoto: picture alliance/AP Photo

Macron ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga matasa masu kananan sana'o'i da yawansu ya kai 300, a rana ta biyu ta ziyarar da ya kai Najeriya yana mai cewa nahiyoyin biyu na da matsala iri guda. Macron ya kuma sha alwashin shawo kan matsalar da kungiyar Tarayyar Turai ke fama da ita kan batun bakin hauren, sai dai ya ce zai kai ga cimma wannan buri nasa ne kawai, da hadin kan kasashen Afirka.