Macron ya kafa sabuwar gwamnatin Faransa
May 17, 2017Talla
Sabon Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kafa gwamnati a karon farko a wannan rana ta Laraba inda ya bayyana fitaccen dan gurguzun nan Jean-Yves Le Drian a matsayin wanda zai jagoranci harkokin kasashen waje da 'yar majalisa daga Kungiyar Tarayyar Turai Sylie Goulard a matsayin ministar tsaro.
Wasu manyan jami'ai da aka nada sun hadar da magajin garin birnin Lyon Gerard Collomb a matsayin ministan harkokin cikin gida sai mai matsakaicin ra'ayi Francois Bayrou da zai kula da harkokin shari'a, da mai ra'ayin rikau Bruno Le Maire da aka bayyana a matsayin ministan tattalin arziki.