Macron ya gana da Yariman na Saudiyya | Labarai | DW | 10.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron ya gana da Yariman na Saudiyya

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kai wata ziyara ta dan lokaci a birnin Ryad na kasar Saudiya a wani mataki na neman yayyafa ruwa a wutar rikicin da ya soma ruruwa a tsakanin Saudiyya da Iran.

Saudi-Arabien Riad Besuch Emmanuel Macron (picture-äalliance/AA/Saudi Royal Council/B. Algaloud)

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron da Yerimen Saudiyya Mohammed Ben Salmane

Yayin da ya kammala ziyarar ta sa'o'i 24 a birnin Dubai na Hadaddaiyar Daular Larabawa ne, shugaban na Faransa ya sanar da ziyarar da zai kai ta sa'o'i biyu a kasar ta Saudiyya domin ganawa da Yerima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed ben Salman, da ke a matsayin babban mai fada a ji a kasar ta Saudiyya.

" Ya na da muhimmanci mu samu tattaunawa mai armashi, na farko domin mu gane dalillan matakan da Saudiyya ke dauka na cikin gida, da kuma abun da ya shafi kasashen yankin kamar batun Iran, da Yemen dangane da rikicin da ke gudana yanzu haka, da kuma illolin da hakan ke yi, sannan akwai matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka kan batun shigar da kayayakin agaji a kasar Yemen, wannan batu yana da babban muhimmanci a garemu kuma batutuwa ne da duk zamu tattauna tare da Yerima mai jiran gado na Saudiyya.

Shugaban na Faransa dai Macron ya samu ganawa da Yariman na Saudiyya Mohammed ben Salman, inda suka tattauna wadannan batutuwa, sai da babu wani bayani na bayan tattaunawar daga bangaran kasar ta Faransa.