Macron na son Ursula ta shugabanci EU
July 2, 2019Talla
Shugaba Emmaneul Macron na Faransa ya shigar da bukatarsa ta nadin Ursula von der Leyen ministar tsaron Jamus a matsayin sabuwar shugabar hukumar Tarayyar Turai.
Emmaneul Macron ya shigar da bukatar ne ga Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus a yayin ci gaba da taron da kungiyar tarayyar Turai ke gudanarwa yanzu haka a kasar Beljiyam, biyo byan dage ci gaba da taron a jiya saboda rashin samun matsaya.
Jaridar Die Welt ta kasar jamus da ke fitowa kowace rana, ta ambato cewa hatta Donald Tusk shugaban hukumar mai barin gado ya bayar da shawarwarin nada Ursula a matsayin shugabar hukumar.