Macron na kammala ziyararsa a Najeriya | Labarai | DW | 04.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron na kammala ziyararsa a Najeriya

A ci gaba da ziyarar da yake a Najeriya, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Lagos cibiyar kasuwancin kasar, inda ya halarci wajen shagalin bikin tuna wakokin Fela Kuti.

Nigeria Abuja Emmanuel Macron und Präsident Muhammadu Buhari (DW/U. Musa)

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Da isarsa birnin na Lagos, Macron ya halarci wani shagalin biki a wajen da ake gudanar da wakokin tunawa da shahararren mawakin nan na Najeriyar da ya yi fice a wakokin afrobeat Fela Kuti. Macron dai ya halarci wannan bikin ne bayan ganawarsa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari inda suka sha alwashin hada karfi da karfe domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a Afirka ta yamma baki daya.