Macky Sall ya kama hanyar yin tazarce | Labarai | DW | 26.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Senegal: Macky sall na gaba a jerin 'yan takara

Macky Sall ya kama hanyar yin tazarce

Shugaban kasar Senegal Macky sall na kan hanyar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tun a zagayen farko.

Shugaban kasar Senegal Macky sall na kan hanyar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tun a zagayen farko.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa Macky sall ya zuwa yanzu yana kan gaba da kuri'u miliyan biyu da dubu dari biyu, idan aka kwatanta da abokan hamayyarsa wadanda kawo yanzu ba su wuce samun kuri'a Miliyan daya da dubu 700 ba.

Tuni wasu kafafen sadarwa na cikin gida da kamfanin dillancin labaran kasar Senegal APS suka ce Shugaban ya kama hanyar yin tazarce karo na biyu a karagar mulki inda ya samu kashi 57 cikin 100 a yayin da shi kuma tsohon firaministan kasar Idrissa  Seck ke biye masa da kashi 15 cikin 100, batun da kawo yanzu hukumar zaben kasar ta bayyana kashi 90 cikin 100 na kuri'un da aka kada.