Mace mai sana′ar gyaran injina a Kano | Himma dai Matasa | DW | 02.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Mace mai sana'ar gyaran injina a Kano

Matashiya Fadila Sani Shu'aibu 'yar asalin unguwar Fagge a birnin Kano ta zama mace mai kamar maza don tana sana'ar gyaran injinan janareta.

Galiban matasa musamman mata da suka yi karatu a nahiyar Afirka ba kasafai suke iya karyar da kai su yi sana'ar hannu domin dogaro da kai ba, yawanci sun fi kaunar makalewa a ofis kodai aikin gwamnati ko kuma aikin kamfani, to amma matashiya Fadila Sani Shu'aibu 'yar asalin unguwar Fagge a birnin Kano ta zama mace mai kamar maza kwari ne babu, domin bayan da ta kammala karatunta aiki bai zo ba, ba ta zauna jiran tsammanin warabbuka ba, sai kawai ta shiga neman aikin yi, domin samun rufin asiri har Allah ya sa ta ji shelar koyar da sana'oin hannu ga matasa da wani kamfani na matashiya ke yi, anan ne ta shiga kuma abin mamaki sai ta zabi koyon gyaran janareta, yanzu haka dai Fadila ta ce Alhamdulillahi domin ta koya ta kuma sami sana'a, ganin cewar gyaran janerata sana'a ce da aka fi kallon ta a matsayin sana'ar maza zalla hakan ma ya sa Fadila ta ce to ita kam wannan sana'a za ta yi.

A dubi bidiyo 01:21

Mace mai gyaran janareta a Kano

Yawancin mutane na kallon sana a irin wannan a matsayin sana'ar gajiyawa amma Fadila ta ce rashin sani ne kan sa karen gwauro ya kori bazawara domin sana'ar ta wanke mata takaici. Nabila ta ce ta ba za ta iya barin aikinta domin neman aikin gwamnati ba domin da wuya ta sami wanda zai share mata hawaye kamar sa ba.

Nabila dai na jan hankalin matasa maza da mata da su zamo masu samar da aikin yi ba masu neman aikin yi ba komai matsayin karatunsu.

 

Sauti da bidiyo akan labarin