Mace-mace a harin bam a Bagadaza
October 27, 2014Talla
Jami'an 'yan sanda a Iraki sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai a Bagadaza ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin goma sha biyar baya ga wasu da dama da suka samu raunuka, wasunsu munana.
Shaidun gani da ido suka ce harin da ya auku dazu kuma an kaishi ne a lardin nan na Karrada da ke da yawan shaguna da gidajen cin abinci inda mabiya tafarkin Shi'a da 'yan Sunni kan gudanar da harkokinsu.
Ya zuwa yanzu dai babu labarin wata kungiya da ta dau alhakin kai wannan harin. Sai dai dama Irakin na fama da hare-hare makamatan wannan, baya ga barazana da take fuskanta daga 'yan kungiyar nan ta IS da ke rajin girka daular Musulunci a Irakin da Siriya.