Mace-mace a haɗarin jirgin sama a Kaduna | Labarai | DW | 29.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-mace a haɗarin jirgin sama a Kaduna

Aƙalla mutane bakwai sun rasa rayukansu bayan da wani ƙaramin jirgin sama ya yi haɗari a Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Da misali karfe bakwai na safiyar Asabar ne jirgin saman kirar Donnier Aircraft ya yi haɗari a kusa da cibiyar horas da sojojin Najeriya na NDA da ke Kaduna. Ba a dai bayyana musabbabin faɗuwar jirgin ba, amma dai na horas da sojoji dabarun tuki ne.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA da sauran ƙungiyoyin agaji sun kai ɗauki don ceto rayukan waɗanda suke cikin jirgin. Sai dai kuma Umar Abdullahi na kungiyar Red Cross ya bayyana cewar ba wanda aka ciroshi da rai.

Sauti da bidiyo akan labarin