Mace-mace a filin kwallon Dakar a Senegal | Labarai | DW | 16.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-mace a filin kwallon Dakar a Senegal

Mutum takwas sun rigamu gidan gaskiya a Dakar babban birnin kasar Senegal a wata turereniya da ta afku bayan barkewar fada tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa da ke gaba da juna.

Ministan wasanni na Senegal ya tabbatar da mutuwar mutan takwas da kuma wasu karin 60 da suka samu raunuka ciki har da wata karamar yarinya. Wannan hadarin ya faru ne a yammacin  Asabar a babban filin wasan kwallon kafa na Demba Diop da ke Dakar, lokacin da ake buga wasan karshe na neman cin kofin kalubale tsakanin kungiyar wasan kwallon kafar US Ouakam da Stade de Mbour.

Rahotanni sun nunar da cewar magoya bayan kungiyoyin biyu sun ta jifar junansu da duwatsu. Sai dai kuma  amfani da hayaki mai sa kwalla da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi ne ya haifar da rudani. Wata katanga ta rifta a lokacin da mutane ke kokawar hawa kanta don tsira daga hayaki mai sa hawaye.

Ita dai kasar Senegal da ke yammacin Afirka tana shan suka dangane da yadda take tinkarar hadarurruka da suka faru a wannan shekarar ciki har da na taron addini a watan Afirilu inda mutane da dama suka rasa rayukansu a wata gobarar da ta tashi.