1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Fafaroma Francis na Krisimeti

Ramatu Garba Baba
December 24, 2018

Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis zai gudanar da addu'o'i da kuma jawabi ga miliyoyin mabiya addini Kirista gabanin soma bukukuwan Krismeti na murnar haihuwa Yesu almasihu.

https://p.dw.com/p/3AbO0
Papst Franziskus Weihnachtssegen Urbi et Orbi 2013
Hoto: Reuters

Wannan na zuwa ne a yayin da a daya bangaren, mataimakinsa Pietro Parolin, ke kai ziyara a kasar Iraki inda nan zai karfafa wa mabiya gwiwa tare da gudanar da bikin na bana da rukunin jama'ar da rikicin ta'addanci ya ta'azzara.

Bisa al'ada, Fafaroma Francis mai shekaru tamanin da biyu zai soma jawabin na sa ne da addu'o'i kafin ya tabo wasu batutuwa da ke ciwa jama'a tuwo a kwarya. Rahotannin sun nunar cewa mabiya darikar Katolika na daga cikin addinai na duniya da suka dandana kudarsu a sanadiyar rikicin ta'addanci da ake samu a sassan duniya.