Mabiya addini Kirista na bikin Kirsimeti | Labarai | DW | 25.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mabiya addini Kirista na bikin Kirsimeti

Paparoma ya nemi samun zaman lafiya tare da kyautata wa 'yan gudun hijira da rikice-rikice suka ritsa da su

Shugaban Kirirstoci mabiya darikar Kotolika Paparoma Francis ya yi amfani da sakon bikin Kirsimeti na wannan shekara kan halin da 'yan gudun hijira suke ciki sakamakon rikice-rikicen da ke ci gaba da ritsawa da wasu sassan duniya.

Dan shekaru 78 da haihuwa, Paparoman ya yi tir da yadda ake samun tashe-tashen hankula da musguna wa tsirarun addinai a wuraren kamar Najeriya da Boko Haram ke kai hare-hare, da yankin Gabas ta Tsakiya, da Ukraine, sannan ya nemi kawo karshen hare-hare kan kananan yara kamar wanda ya faru a kasar Pakistan.

Mabiya addini Kirista na ci gaba da shagulgular bikin na Kirsimeti.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar