1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mabambamtan ra'ayoyi ga mulkin Hamid Karzai

April 5, 2014

Yayin da al'ummar Afghanistan suka kada kuri'a a zaben sabon shugaban kasa da zai maye gurbin Karzai, ra'ayi ya bambamta game da salon mulkin shugaban mai barin gado.

https://p.dw.com/p/1BcaI
Loja Dschirga 21.11.2013 Kabul Karsai Rede
Hoto: Reuters

A cikin yanayi na tashe-tashen hankula, a wannan Asabar masu zabe kimanin miliyan 12 a Afghanistan sun kada kuri'a a zaben sabon shugaban kasa da zai maye gurbin shugaba mai barin gado Hamid Karzai, wanda bayan wa'adin shugabanci karo na biyu doka ta hana masa sake tsayawa takara.

Hamid Karzai ya kasance mutumin da aka dora wa nauyin gudanar da aikin sake gina Afghanistan bayan kawo karshen mulkin danniya ta 'yan Taliban na tsawon shekaru shidda. A cikin watan Disamban 2001 aka nada shi shugaban gwamnatin rikon kwarya a gun taron kasa da kasa kan Afghanistan da ya gudana a nan birnin Bonn. Yana daya daga cikin masu fada a ji kalilan a Afghanistan da babu jini a hannunsu wanda kuma ke da kyakkyawar dangantaka da Amirka.

A cikin shekaru 12 na mulkinsa, ana iya cewa Karzai ya cimma wani ci gaba in banda manyan matsaloli guda biyu wato yaki da cin hanci da rashawa da kuma manufofinsa na ketare musamman dangane da kasar Pakistan.

Pakistan Islamabad Nawas Sharif und Hamid Karsai Afghanistan Treffen Politik
Tsamin dangantaka duk da masafaha. Karzai da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif a Augustan 2013Hoto: AFP/Getty Images

Adrienne Woltersdorf shugabar gidauniyar Friedrich-Ebert a Afganistan na mai ra'ayin cewa Karzai ya taka rawar gani.

"Ya yi kokari ya dare kan karagar mulki tsawon shekaru 10 a kan wani mukamin siyasa mafi wahala da ba a taba samun irinsa a doron kasa ba."

Saboda haka bai kamata a raina wannan aiki a wata kasa mai fama da rigingimu ba. Ya yi kokarin daidaita lamuran siyasar kasar, inda kuma ya rika kiran masu tayar da kayar baya 'yan'uwansa 'yan kasa don nuna kusanci da su. A zamanin mulkinsa an samu karuwar yawan yara mata da ke shiga makaranta, sannan an gina sabbin jami'o'i an kuma farfado da tsofaffi yayin da tashoshin rediyo da na telebijin suka kirkiro da shirye-shirye masu kayatarwa.

Kasashen yammam sun dan juya masa baya

Sai dai ba a jima ba farin jinin Karzai ya fara dushewa, inda 'yan kasar ke zarginsa da zama karen farautar kasashen yamma. Yayin da a zabensa na farko a shekarar 2004 ya samu gagarumar nasara, amma ya sake lashe zaben wa'adi na biyu albarkacin magudi da aringizon kuri'u. Sannan halin tsaro ya tabarbare sakamakon hare-haren 'yan Taliban, kana yardar da ake wa Amirka ta ragu.

Obama beim Überraschungsbesuch in Afghanistan Mai 2012
Huldar tsaro mai tattare a cikas. Obama da Karzai a Kabul cikin watan Mayun 2012Hoto: Reuters

Winfried Nachtwei masani kan harkokin tsaro da zaman lafiya ya ce kasashen yamma ma na da nasu laifi game da tabarbarewar tsaro a Afghanistan.

"An yi ta dora laifin a kan 'yan Afghanistan musamman ma shugaban, amma an manta cewa a shekarun farko na mulkinsa, kasashen yamma sun kai shi sun baro."

Da kyar da gumin goshi Karzai ya shawo kan kungiyar kawance tsaron NATO ta girke dakaru don tabbatar da tsaro a yankunan da ke nesa da birnin Kabul.

Ci gaba a wasu bangarori na rayuwa

Duk da matsalolin tsaro da har yanzu kasar ke fuskanta, 'yan Afghanistan da yawa na yaba masa ga irin ci gaban da ya samu a shekarun farko na mulkinsa, musamman a bangaren 'yancin mata da na 'yan jarida da kuma 'yancin kada kuri'a, sai dai bai cika alkawuran da ya dauka ba. Waheeda Shujayee mai shagon sayar da tufafi ne a Kabul.

Afghanistan Mazar Präsidentschaftswahl 2014
Mutane maza da mata sun fita kwansu da kwarkwata don kada kuri'aHoto: DW/N.Asir

"'Yan Afghanistan sun yi murna ganin an kifar da Taliban kuma an samu shugaba mai sassaucin ra'ayi. Amma gaba daya sha'anin tsaro da kuma tattalin arzikin kasa suka tabarbare. Hakan ya sa 'yan kasar da dama sun yi kaura. Mun yi fatan samun ci gaba mai ma'ana."

'Yan takarar neman shugabancin kasar a zaben na ranar Asabar sun ce za su sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da Amirka kana za su zauna kan teburin shawarwari da 'yan Taliban a yunkurin sanya dukkan 'yan Afghanistan cikin harkokin tafiyar da kasar.

Mawallafa: Waslat Hasrat-Nazimi / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo