1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na kan siradi da makaman nukiliya

Abdullahi Tanko Bala
February 25, 2020

Kasashen Sweden da Jamus sun bukaci kawo karshen kiki-kaka kan shirin kwance damarar makaman nukiliya yayin da ake fargabar karuwar barazanar tsaro a duniya.

https://p.dw.com/p/3YPoX
Schweden Ministertreffen zur nuklearen Abrüstung in Stockholm
Hoto: Getty Images/AFP/C. Bresciani

Mambobin kasashe da ke cikin shirin aniyar kwance damarar makaman sun gudanar da taro a Berlin domin samar da masalaha tsakanin kasashe da suka mallaki makaman nukiliya da kuma wadanda basu mallaka ba, gabanin taron kolin da za a gudanar domin sake nazarin yarjejeniyar kwance damarar makaman nukiliyar a watan Afirilun 2020.

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas yace duniya na kan siradi inda ya bada misali da janyewar Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran da kuma kawo karshen matsakaitan makaman nukiliya tsakanin Rasha da Amirka. 

"Yace muna so mu kawo karshen wannan kiki-kaka kan makaman nukiliya,duniya na kan siradi. A shekarar 2018 Amirka ta janye daga yarjejeniyar Vienna kan makaman nukiliya wadda aka fi sani da yarjejeniyar nukiliyar Iran. Sannan a 2018 an rasa wata dama saboda janyewar Rasha daga yarjejeniyar matsakaitan makaman nukiliya. Idan aka cigaba akan wannan tafarki to kuwa labbuda ana cikin hadari na tabarbarewar tsaro a duniya baki daya".